Malaman makaranta sun tsunduma yajin aiki a Iran

Kungiyar Malaman Makaranta ta Iran ta fitar da sanarwa ta shafinta na sada zumunta na yanar gizo inda ta ce, ta tsunduma yajin aiki a garuruwan aksar da suka hada da: Tahran, Tebriz, Meşhed, Isfahan, Şiraz, Hemadan, Merivan, Kermanşah, Iylam da Yasuc.

Sakamakon tafiya yajin aikin da malaman suka yi, ya sanya dalibai ba sa zuwa makaranta.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a kwanakin baya ta ce, sakamakon tsadar rayuwa a Iran sun umarci mambobinsu da kar su shiga azuzuwa a ranakun 14 da 15 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta kuma bukaci da a kara yawan albashin ma'aikata, kyautata yanayin aikinsu tare da kawo karshen kama su da daure su da ake yi a kasar.Labarai masu alaka