Sai a watan 6 aka sanya hannu kan kasafin kudin bana a Najeriya. Laifin waye?

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2017 wata 1 bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da shi wanda ya kama dalar Amurka biliyan 24.3.

Osinbajo ya sanar da cewa “Na sanya hannu kan kasafin kudin na Najeriya na 2017 bisa tsarin gina tattalin arzikinmu da shugaba Muhammadu Buhari ya assasa a watan Afrilu.”

Mukaddashin shugaban na Najeriya ya kuma gode wa majalisar dokokin kasar kan wannan batu.

Ya ce, ana gaf da samun walwala a kasar bayan an sha fama da matsalar karyewar tattalin arziki.

AALabarai masu alaka