Matsalar Fari: Sarkin Morokko zai jagoranci Sallar rokon ruwa a kasar

Sarkin Morokko Muhammad na 4 ya yi kira da a gudanar da Sallar Rokon Ruwa a ranar Juma'a sakamakon matsalar fari da kasar ke fuskanta tsawon lokaci.

Ana yin Sallar Rokon Ruwa da nufin Allah Madaukakin Sargi Ya yi wa a'uma Afuwa tare da saukar musu da ruwan sama.

Sanarwar da Ma'aikatar Kula da Harkokin Addini suka fitar ta ce,  za a gudanar da Sallar Rokon Ruwa a dukkanin Masallatan Juma'a da ke fadin kasar Morokko.

Ministan Aiyukan Noma da Kiwo na Morokko Aziz Akhannouch ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar a ranar Litinin inda ya bayyana damuwarsa game da halin da aka shiga na matsalar fari.

Ya ce, an samu karancin ruwan sama da kaso 74 cikin 100 a fadin kasar ta Morokko.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta fara daukar matakan rage radadin da jama'a ke ji.Labarai masu alaka