Jirgin ruwa ya kife a China inda aka nemi mutane 12 aka rasa

An samu nasarar kubutar da mutane 14 inda wasu 12 suka bace sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a kasar China.

Jirgin ruwa ya kife a China inda aka nemi mutane 12 aka rasa

An samu nasarar kubutar da mutane 14 inda wasu 12 suka bace sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a kasar China.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar da labarin cewa, wasu jiragen ruwa 2 ne suka yi karo a wani kogi da ke kusa da garin Guanjou na jihar Guangdong.

Jirgin ruwan da ke dauke da yashi ne ya kife sakamakon hatsarin.

Mahukuntan jihar Guangdong sun ce, a aikin ceton da aka fara an kubutar da mutane 14 inda ake ci gaba da neman wasu 12 da suka bace.

Ana kuma ci gaba da binciken musabbabin hatsarin.Labarai masu alaka