An gano wata sabuwar hanyar magance sanko

A wani bincike da aka gwada a kan beraye a Koriya ta kudu an samu nasarar ganon hanyar magance matsalar sanko da ke damun maza.

An gano wata sabuwar hanyar magance sanko

A wani bincike da aka gwada a kan beraye a Koriya ta kudu an samu nasarar ganon hanyar magance matsalar sanko da ke damun maza.

A jami'ar Yonsei da ke birnin Seoul aka gudanar da binciken inda aka yi amfani da beraye kuma a tsawon kwanaki 28 aka samu sakamako mai kyau.

Sabuwar dabarar za ta magance matsalar sanko inda gashi zai dinga fitowa yadda ya ke sosai.

Farfesa Kang-Yell Choi ya ce, sabon sinadarin PTD-DBM da za a dinga amfani da shi zai dinga magance matsalar zubar gashi da kuma mutuwar fata.Labarai masu alaka