Mutum-Mutumi za su janyo mutane miliyan 800 su rasa aiyukansu nan da shekarar 2030

Nan da shekarar 2030 mutane miliyan 400-800 ne za su rasa aiyukansu sakamakon ci gaba da samar da mutum-mutumi da ake yi.

A binciken da Cibiyar McKinsey Global ta gudanar kan sana'o'i 800 a kasashen duniya 46 ta gano cewa, saka mutum-mutumi aiki da ake yi na janyo kowanne mutum 1 cikin mutane 5 ya rasa aiki a duniya.

Binciken ya ja hankali da cewa, za a fi amfani da mutum-mutumin a kasashen duniya da suka ci gaba, sakamakon haka a nan ne za a fi fuskantar rasa aiyukan yi..

Ra hoton ya ce, a kasashen da za a fi rasa aiyukan akwai Jamus da Amurka da wasunsu inda lamarin zai shafi mutum 1 a cikin kowanne mutum 3.

Binciken ya ce, ya kamata kafin a sanya mutum-mutuman aiki kasashe su fara zuba jari a wasu bangarorin ta yadda jama'arsu za su sami aiyukan yi.Labarai masu alaka