• Bidiyo

Turkiyya ta mika wa Falasdinawa gidaje 320 da ta gina musu a Zirin Gaza

Hukumar Hadin Kai Da Cigaba ta Turkiyya TIKa ta mika mukullan gidaje 320 ga Falasdinawa wadanda ta gina a Zirin Gaza.

Turkiyya ta mika wa Falasdinawa gidaje 320 da ta gina musu a Zirin Gaza

Hukumar Hadin Kai Da Cigaba ta Turkiyya TIKa ta mika mukullan gidaje 320 ga Falasdinawa wadanda ta gina a Zirin Gaza.

Ministan Muhalli da wajen zama na Falasdin Mufid Al-Hasayine ya yi jawabi a wajen bikin mika mukullan gidajen inda ya ce, TIKA ta gina gidajen ne ga mutanen da Isra'ila ta rushe wa matsugunai a shekarar 2014 bayan kai musu hare-hare.

Hasayine ya yi fatan alheri ga iyalan da aka gina wa gidajen a yankin.

Ministan ya kuma yaba tare da gode wa Turkiyya bisa wannan aiki na alheri da ta yi.

Bayan jawabin na Hasayine an mika mukullan gidajen ga daruruwan Falasdinawa.

Kowanne gida yana da girman mita 100 inda adadin mutane kusan dubu 2 da 250 za su zauna a cikinsu.Labarai masu alaka