An daure Yariman Saudiyya a gidan maza

An tura Yariman saudiyya Al-Walid bin Talal zuwa gidan maza wanda yana daya daga cikin manyan masu kudin Masarautar Saudiyya.

An daure Yariman Saudiyya a gidan maza

An tura Yariman saudiyya Al-Walid bin Talal zuwa gidan maza wanda yana daya daga cikin manyan masu kudin Masarautar Saudiyya.

An kama Yarima Talal ne watanni 2 da suka wuce bayan fara farmakin kama masu aikata cin hanci da rashawa a kasar.

An amince da tura Yariman gidan kaso bayan ya ki amince wa da ya biya kasar ta Saudiyya Yuro miliyan 728 inda aka kai shi gidan kurkukun Al-Ha'ir.

A baya dai yana zaune a otel din da aka tsare shi tare da manyan mutanen da aka kama.

An kama mutane 200 a Saudiyya bayan fara kamen wasu manyan Yarimomi da Ministoci a wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.



Labarai masu alaka