Turkiyya za ta samar da makami mai linzami mai tafiyar dogon zango

Kamfanin Kayan Lantarkin Sojoji ASELSAN, Kamfanin Samar da Makamin Roka Da Sayar da shi ROKETSAN, Hukumar Kimiyya da Fasahar Kere-Kere ta Turkiyya TUBITAK tare da hadin gwiwar Hukumar Bayar da Shawara Kan Tsaro ta kasar za su samar da makami mai linzami.

Turkiyya za ta samar da makami mai linzami mai tafiyar dogon zango

Kamfanin Kayan Lantarkin Sojoji ASELSAN, Kamfanin Samar da Makamin Roka Da Sayar da shi ROKETSAN, Hukumar Kimiyya da Fasahar Kere-Kere ta Turkiyya TUBITAK tare da hadin gwiwar Hukumar Bayar da SHawara kan Tsaro ta Turkiyya za su samar da makami mai linzami kirar kasa da ka iya yin tafiyar zango mai nisa.

Sanarwar da aka fitar a dandalin sanar da jama'a na kamfanin ASELSAN ta ce, a karkashin yarjejeniyar ASELSAN zai bayar da Lira miliyan 869 da dubu 13 da 861 da kuma Yuro miliyan 257 da dubu 600.

Za a kammala aikin a shekarar 2021 tare da mika wa Turkiyya makaman.Labarai masu alaka