An kashe tsuntsaye miliyan 25 a Iran saboda bullar murar tsuntsaye

Kamfanin dillancin labarai na ILNA ya bayyana cewa, an kashe tsuntsaye da dangoginsu da ale kiwo a gidajen gona kimanin miliyan 25 a Iran sakamakon bullar cutar murar tsuntsaye.

Shugaban Kungiyar masu kiwon kaji da tsuntsaye da sayar da kwai na Iran Nasir Nabipur ya bayyana cewa, an kashe tsuntsayen da suka kai kaso 40 na adadin da ake da su a Iran domin tsare lafiya da rayukan jama'ar jasar.

Ya ce, sakamakon kashe tsauntssye ya sanya karancin samu  kwai wanda hakan ya sanya farashinsa tashi matuka.

Iran na shigar da kwai daga Turkiyya kusan tirela dubu 50 a kowacce shekara sakamakon yawan samun murar tsuntsaye a kasar.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta ce, daga shekarar 2003-2018 mutane 454 cutar murar tsuntsaye ta kashe a duniya baki dayaLabarai masu alaka