Shin EFCC za ta binciki macijin da ya hadiye Naira miliyan 36 a Najeriya?

A karshen makon da ya gabata ne kafafan yada labarai a Najeriya suka rawaito yadda a jihar Benue da ke tsakiyar kasar hukumomi suka bayyana cewa, wani kasurgumin maciji ya hadiye Naira Miliyan 36 na sayar da katin zana jarrabawar neman shiga jami'a JAMB.

A wani sako da Hukumar Yaki da Cin hanci da Almundahana ta Najeriya EFCC ta fiytar a shafinta na Twitter ta nuna wata mikiya da ta danne maciji inda aka bayar da sakon cewa, mikiyar ba za ta tausaya wa macijin da ya hadiye Naira miliyan 36 a Najeriya ba.

Najeriya dai kasa ce bai dimbin arziki amma kuma cin hanci, rashawa, da almundahana da kudaden gwamnati ya sanya kasar ke fuskantar matsaloli da dama.

A shekarun 2000 ne tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kafa Hukumar EFCC domin yaki da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

Amma ana yawan zargin hukumar da farautar 'yan adawa da gwamnatin da ke kan mulki.

Hukumar dai a halin yanzu ta gurfanar da mutane da dama a gaban kotuna daban-daban da ke kasar bisa zarginsu da warure dukiyar kasa.

'Yan Najeriya dai na zuba ido su ga yadda Hukumar za ta binciki batun macijin da aka ce ya hadiye Naira miliyan 36 a jihar ta Benue.Labarai masu alaka