Sabbin matakan habaka Tattalin Arziki da Turkiyya ke dauka

Kasancewar albarkatun dake yankin da Turkiyya ta ke, sun sanya masu saka hannayen jari fa’idantuwa da ababe da dama. Ya kamata mu yi nazari akan waɗannan damar da kuma yadda masu saka hannayen jari ciki da waje zasu iya amfana da kuma yadda lamarin zai ƙa

Sabbin matakan habaka Tattalin Arziki da Turkiyya ke dauka

Kasancewar albarkatun dake yankin da Turkiyya ta ke, sun sanya masu saka hannayen jari fa’idantuwa da ababe da dama. Ya kamata mu yi nazari akan waɗannan damar da kuma yadda masu saka hannayen jari ciki da waje zasu iya amfana da kuma yadda lamarin zai ƙara bunƙasa.

Mun kasance tare da ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL dake sashen nazarin tattalin arziki a jami'ar Yıldırım Beyazıt anan Turkiyya.

Turkiyya na samar da damar saka hannun jari ga kasashen waje dangane da irin ci gaban da ƙasar ke da shi. Duk da ana ganin kamar damar tafi yawa ga ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, ƙananan ƙasashe ma nada fannoni da zasu iya saka hannayen jari a ƙasar.

Turkiyya wacce ke cikin ƙasashe masu tasowa ta yi nasarar inganta lamurkan saka hannun jari daga ƙasashen waje a cikin shekaru 15 da suka gabata. A yayinda ƙasar ta samu hannun jari na dala biliyan 15.1 a cikin shekaru 50 tsakanin 1950-2001, a cikin shekarun 2002-2017 kuwa ta yi nasarar nunka hannun jarin har sau 12 a yayinda hannayen jarin suka kai dala biliyan 191.1.

Domin ƙara bunƙasa wannan nasarorin da aka samu a cikin shekaru goma sha biyar, an fitar da wasu sabbin tsaruka da dama. Waɗannan sabbin tsarukan zasu sanya ƙasar ta cimma burinta akan haɓakar da lamurkan saka hannun jari a ƙasar.

Duk ƙasar da ke buƙatar bunƙasa lamurkan hannun jarinta, ya zama wajibi ta samar da wasu dama da kuma lamurkan da zasu sauwaƙa lamurka ga masu sanya hannu jarin daga ƙasashen waje, hakan ne zai janyo su izuwa ƙasar domin ƙara saka hannun jarin.

Turkiyya ta ɗauki matakan tabbatar da sauwaka aiyukan ƙasar, a yayinda take ta 60 a duniya akan jerin ƙasashen da ke gudanar da aiyuka cikin sauki, tana kuma aniyar kasance wa ta 20 anan gaba.

Idan Turkiyya ta yi nasarar kasance wa cikin ƙasashe 20 dake sauwaka aiyuka a duniya, lamurkan saka hannun jari a ƙasar zai bunƙasa inda za ta fara gwagwarmaya da manyan ƙasashe.

Waɗanan sabbin tsarukan da ɗaya daga cikin mataimakan Firaministan Turkiyya Recep Akdağ ya bayyana da zasu ɗauki watanni biyar ana gudanar da su, sun samu goyon bayan masanar hannun jari daga bankin duniya da kuma manyan ƴan kasuwa.

Turkiyya dai ta ɗauki matakan warware dukkannin matsaloli dake ƙalubalantar lamurkan saka hannun jari a ƙasar, sabili da haka a iya samun inganci a fannin da dama.

Ya kamata mu dubi ababen da waɗannan sabbin tsarukan su ka kunsa. Da farko dai Ma'aikatan da ke kula da kafa kanfuna zasu sauwaka lamurkan buɗe kanfanoni a ƙasar, a yayinda ake da niyyar rage ƙaidojin kafa kanfuna daga bakwai zuwa daya ɗilo.

A ɗayan barayin kuma za'a aiyanar da sabbin tsaruka akan bayar da bashi wanda babu irin sa a sauran ƙasashen duniya. A maimakon cire ƙara lokacin biyan bashi za'a samar da wasu ƙaidoji da za su kuɓutar da waɗanda suka ka sa biyan basussuka. Haka kuma za'a rage wa'adin biyan basussuka na shekaru 7-8 da kusan watanni 23.

Haka kuma za'a rage ƙaidojin izinin yin gina a ƙasar daga 12 zuwa 5, a yayinda wasu ƙaidojin 18 za'a rage su zuwa 6. Za'a ɗauki waɗannan matakan ne domin sauwaka lamurkan gina a ƙasar.

Waɗannan kaɗan daga cikin muhimman matakai 93 da Turkiyya za ta ɗauka domin inganta lamurkan saka hannun jari ne. Ko shakka babu waɗannan matakan za su kauda dukkan ƙalubalolin da ke daƙile harkokin saka hannun jari a ƙasar. Da hakan, ƙasar za ta cimma burinta na habbaka lamurkan saka hannun jari da ma tattalin arzikinta gaba ɗaya.

Wannan sharhin ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL ne malami a jami'ar Yıldırım Beyazıt anan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka