Alakar Turkiyya da Afirka na kara habaka

A halin yanzu Turkiyya ta soma ƙaddamar da shirin hurɗa da nahiyar Afirka ta fannoni dabam- dabam, inda ta aiyanar da sabbin tsarukan dangantaka da nahiyar akan tsarin bada gudunmawa, hurɗar diflomasiyya da kuma lamurkan ci gaban dukkan bangarorin.

Alakar Turkiyya da Afirka na kara habaka

Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sanya Turkiyya yin nasara a hurɗa da nahiyar Afirka shi ne, kasancewar Turkiyya ƙasa wacce bata taɓa aiyanar da mulkin mallaka ba kuma tana gudanar da hurɗa tsakaninta da nahiyar ne akan tafarkin dai-daita.

A ƴan kwanakin da suka gabata, ziyartar da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya kai a ƙasashen Afirka da suka haɗa da Algeriya, Muritanya, Senegal da Mali mataki ne dake nuna irin bunƙasar hurɗar diflomasiyya, kasuwanci da tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu.

Akan wannan maudu'in mun kasance tare da malam Can ACUN dake Cibiyar Binciken Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA anan Turkiyya.

Hadahadar kasuwanci tsakanin Turkiyya da nahiyar Afirka ya nunka sau shidda a cikin shekaru goma sha biyar a yayinda da cinikayyar ta kai ta dala biliyan 17.5. A yayinda hannayen jarin da Turkiyya ta saka a Afrika yake dala miliyan 100 a shekarar 2003, a shekarar 2017 sun haura har zuwa dala biliyan 6.5. A ziyarar kwanan nan da shugaba Erdoğan ya kai Afirka ma ya rataɓa hannu akan yarjejeniyoyin kasuwanci da tattalin arziki da dama da wasu ƙasashen Afirka. An bayyana cewar wannan lamari zai bunƙasa kasuwanci tsakanin bangarorin biyu, a misali, a yayinda kasuwanci tsakanin Turkiyya da Senegal ya kai na dala miliyan 250, an ƙaddamar da aniyar bunƙasar da kasuwancin zuwa dala miliyan 400.

Hurɗar da Turkiyya ke ƙullawa a Afirka ya saɓawa irin na ƙasashen da suka aiyanar da mulkin mallaka a nahiyar. Turkiyya tana gudanar da dangantakarta da nahiyar akan yadda dukkanin bangarorin zasu amfana. A lokacin da shugaba Erdoğan yakai ziyara a Algeriya inda ya yi tsokaci akan daular Usmaniyya da ya bayyana cewar suna tambayar ko Daular Uthmaniyya ta kasance wacce ta aiyanar da mulkin mallaka a Algeriya? Shugaba Erdoğan ya bayyana cewar da haka ne, ai da wannan tambayar da harshen Turkanci za'a tambaye ni bada Faransanci ba. Hakan na nuni ga yadda Turkiyya ke hurɗa da nahiyar Afirka saɓanin irin na ƙasashen da suka mamayi nahiyar.

Daga cikin lamurkan da suka sanya manufar Turkiyya nasara a Afirka su ne bada tallafi da gudunmowa. Turkiyya ta kasance wacce tafi bada kasho mai tsoka ga tallafawa daga cikin kuɗaɗen shigarta a shekara. Hakan na nuni ga yadda ƙasar ke bada muhimmanci akan hurɗarta da sauran ƙasashe. Turkiyya da ta kasance tana taimakawa domin kauda fari, yunwa da talauci, ta kasance akan gaba a ɗaukar matakan inganta rayuwar waɗanda suka samu kansu cikin ƙaƙa-nikayi a sanadiyar ɓarkewar yaƙi da kuma marasa lafiya.

Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya Amina Recep Tayyip Erdoğan ta bayyana shirin bunkasa rayuwar ɗan adam ɗin Turkiyya a takaice, inda take cewa “Fari ka iya zama muƙaddari a Afirka, amma mutuwa a dalilin yunwa ba muƙaddari bane, kissar gilla ma ba muƙaddari bane.( Inda ta ƙara da cewa: )Mun ɗaura ɗamarar samar da lumana da bunƙasar Afirka ta hanyar janyo hankalin ƙungiyoyin ƙasashen duniya akan lamarin”

Baya ga bayar da tallafi ga al'umma; daga cikin hukumomin da suke taka rawar gani a fagen bunƙasar da dangantakar Turkiyya da Afirka sun hada da ma'aikatan tsaro, tattalin arziki, ci gaba, ilimi, hukumar AFAD, ma'aikatan makarantun gaba da sakandare watau YOK, Hukumar bayar da agaji, hukumar bayar da tallafi ga ɗaliban ƙasashen waje da kuma Cibiyar Yunus Emre. Baya ga muhimman aiyukan da wasu ma'aikatun Turkiyya ke gudanar wa a Afirka akwai kuma ƙungiyoyin ƙasar masu zaman kansu da suke aiyanar da aiyuka da dama. Dangantaka dai tsakanin Turkiyya da Al'ummar Afirka na daɗa ƙara kwari a koda yaushe.

A ɗayan barayin kuma, dangane da hurɗar tattalin arziki, Turkiyya na gudanar da gine-gine a Afirka. Kanfunan Turkiyya da dama sun samu tagomashi a fagen aiyanar da aiyuka a nahiyar. A lokacin da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya ziyarci Afirka ya zagayi wuraren da kanfunan Turkiyya ke gudanar da aiyuka dabam-dabam a wasu ƙasashen nahiyar Afirka.

Daga cikin lamurkan da suka tabbatar da gwaɓin dangantakar Turkiyya da nahiyar Afirka shi ne kasancewar yadda aka rufe makarantun kungiyar ta'addar FETO da wasu ma'aikatunsu a wasu ƙasashen Afirka, aka kuma amince da miƙa su ga Hukumar Maarif. Wannan Hukumar Maarif mallakar gwamnatin Turkiyya, yanzu haka tana da makarantu 88 da take ilimantar da yara a ƙasashen Tanzania, Sudan, Somaliya, Sierra Leone, Sao Tome and Principe, Senegal, Niger, Moritanya, Mali, Jamhuriyar Kongo, Gineu, Gambiya, Chad, da Jubuti.

Wannan sharhin Malam Can ACUN ne dake Cibiyar Bincike akan Tattalin Arziki da Siyasa watau SETA dake Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka