Isra'ila ta fara zaluntar Kiristocin yankunan da ta mamaye a Gabashin Kudus

Gwamnatin Isra'ila ta fara sanya haraji da ya wuce tunanin mutane kan kadarorin kiristoci da suka hada da Majami'u a yankin gabashin Kudus da suka yi kaka gida a cikinsa.

Isra'ila ta fara zaluntar Kiristocin yankunan da ta mamaye a Gabashin Kudus

Gwamnatin Isra'ila ta fara sanya haraji da ya wuce tunanin mutane kan kadarorin Kiristoci da suka hada da Majami'u a yankin gabashin Kudus da suka yi kaka gida a cikinsa.

Sakatare Janar na Kungiyar Musulmai-Kiristoci don kare wurare Masu Tsarki Hanna Isah ya bayyana cewa, a yanzu Isra'ila na son kusan dala miliyan 190 daga hannun Majami'un da ke Gabashin Kudus wanda ba abu ne mai yiwu wa ba.

Isa da ya ke Kirista kuma malami a sashen koyon aikin lauya na jami'ar Birzeit ta kasa da kasa ya ce, binciken da suka yi ya gano cewa, kaso 29 na gine-ginen da ke gabashin Kudus mallakar Musulmai ne yayinda kaso 28 kuma ya ke mallakar Kiristoci.

Isah ya kara da cewa, akwai gidajen otel, makarantu, shaguna, filaye da gidajen otel mallakar Majami'un yankin.

Isra'ila dai ta fi zaluntar Falasdinawa Musulmai da ke Gabashin Kudus amma a 'yan kwanakin nan ta jiyo kan Kiristoci.Labarai masu alaka