Turkiyya ta fara fitar da kaji zuwa Japan

Kasar Turkiyya ta fara fitar da kaji zuwa kasar Japan a yayinda  aka fitar da ton 500 da suka kunshi kwantaina da dama.

Turkiyya ta fara fitar da kaji zuwa Japan

Kasar Turkiyya ta fara fitar da kaji zuwa kasar Japan a yayinda  aka fitar da ton 500 da suka kunshi kwantaina da dama.

Ministan harkokin tattalin arzikin Turkiyya Nihat Zeybekci da ya ziyarci Japan ya gana da 'yan kasuwa da takwaransa na kasar Japan a ofishin jakadancin Turkiyya dake Tokyo.

A ganawar an tattauna akan hurdar kasuwancin kasashen biyu tun daga shekarar 2014 har izuwa yau, a yayinda ake shirin aiyanar da taron kasuwanci kashi na tara tsakanin kasashen biyu.

Zeybekci, ya bayyana cewar yanzu haka ana cinikin dala biliyan 4,7 tsakanin kasashen ana kuma fatar nunka hakan sau 4-5.

Inda ya kara da cewa "Muna mutunta Japan, Ina yakini da a shekarar 2018 kasashen biyu zasu kasance masu ingantacciyar hurdar tattalin arziki"

 Labarai masu alaka