An yi zanga-zangar neman kare gurbatar yanayi a jihar Rivers ta Najeriya

Masu zanga-zanga a Fatakwal Babban Birnin Jihar Rivers sun yi zanga-zanga tare da neman gwamnatin Najeriya da ta dauki matakin magance yaduwar wani bakin sinadarin da ke cutar da lafiyar mutane sakamakon aiyukan.

Shekaru 2 da suka gabata ne wasu bakaken abubuwa kanana suka fara yawo a cikin iska a jihar.

Jama’ar jihar ta Rivers sun ce, lamarin na afkuwa ne sakamakon rushe matatun man fetur da ba sa bisa ka’ida a jihar.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sakonsu ga gwamnatin Tarayyar da ta jiha shi ne, a gaggauta kawo karshen wannan matsala wadda ta ke cutar da lafiyarsu.

Sun bayyana cewa, sun bukatar shakar iska mai kyau tare da yanayi ingantacce.

Gwamnatin Najeriya kuma ta bayyana cewa, tana kokarin shawo kan matsalar inda ta fara aiyuka da kwararru dakuma ma’aikatan lafiya.Labarai masu alaka