Erdoğan ya sauka a sabon filin tashi da saukar jiragen sama da Turkiyya ta gina a Istanbul

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi sauka ta farko da jirgin sama samfurin "TC-ANK" a sabon filin tashi da saukar jiragen sama na 3 da aka gina a birnin Istanbul.

istanbul yeni havalimani3.jpg
istanbul yeni havalimani2.jpg
istanbul yeni havalimani1.jpg

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi sauka ta farko da jirgin sama samfurin "TC-ANK" a sabon filin tashi da saukar jiragen sama na 3 da aka gina a birnin Istanbul.

Jirgin na "TC-ANK" ya sauka a titin farko da aka kammala mai tsayin mita dubu 3,750 da fadin mita 60.

Ministan Sufuri na Turkiyya Ahmet Alparslan tare da matukan jirgi da sauran ma'aikata ne suka tarbi shugaba Erdoğan.

Ma'aikatar kashe gobara kamar yadda aka saba sun yi wa jirgin da Erdoğan ya sauka da shi wanka. Daga baya jirgin ya wuce karkashin motocin 'yan kwana-kwana guda 2.

Shugaba Erdoğan ya yi godiya ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmowa a aikin sabon filin jirgin da babu irin sa a nahiyar Turai.

Erdoğan ya ce, a ranar 29 ga watan Oktoba bangaren farko na filin jirgin zai fara akin jigilar fasinjoji.

Za a kammala bangaren farko a watanni 42 kuma a kowacce rana jirage dubu 3,500 za su sauka tare da tashi. 

A cikin filin kjirgin akwai wajen shakatawa mai girman mita dubu 100, wajen ajje motoci dubu 25, wajen ajje kaya mai girman kilomita 42, gadojin fasinjoji 143, wajen kayan cargo na tan miliyan 5.5 da wajen tsaro na kilomita 42.

ıdan aka gamaaikin, filin jirgin zai tara wa Turkiyya Lira biliyan 73 tare da samar da aiki ga mutane dubu 225.Labarai masu alaka