An kashe 'yan ta'addar PKK 60 cikin mako 1 a Turkiyya

An kashe 'yan ta'addar PKK 60 a hare-haren da jami'an tsaron Turkiyya suka kai musu a cikin mako dayan da ya gabata.

An kashe 'yan ta'addar PKK 60 cikin mako 1 a Turkiyya

An kashe 'yan ta'addar PKK 60 a hare-haren da jami'an tsaron Turkiyya suka kai musu a cikin mako dayan da ya gabata.

An kai farmakai kan 'yan ta'addar a lardunan Şırnak, Hakkari, Diyarbakır, Bingöl, Elazığ, Mardin da Siirt.

An kuma kwace makamai da abubuwan fashe wa daga hannun 'yan ta'addar.

Jami'an tsaron sun kuma rusa wuraren buya, mafaka da ma'ajiyar makaman 'yan ta'addar.

A farmakan da aka don dakile hanyar da 'yan ta'addar ke samun kudi an kwace tabar wiwi, da sauran kayan maye da yawa.

haka zalika an kama mutane dubu 5,617 da suka yi kokarin tsallaka iyakar Turkiyya ba bisa ka'ida ba.Labarai masu alaka