Hare-Haren Reshen Zaitun da Manufofin Turkiyya a bangaren Tsaro

Jama'a barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin manufar Turkiyya a kasashen Ketare.

Hare-Haren Reshen Zaitun da Manufofin Turkiyya a bangaren Tsaro

Kamar yadda muka sani, Turkiyya na ci gaba da gwagwarmayar kawar da ta’addanci babu sani babu sabo,inda a yanzu haka ta fara kaddamar da hare-haren “Reshen Zaitun”, da zummar da fatattakar ‘yan ta’addar da suka yi kaka gida, a gaf da iyakokinta, a garin Afrin na kasar Sham.

A wannan makon, duba da hare-haren “Reshen Zaitun” zamu nazarci tsare-tsaren kasar Turkiyya dangane da lamarin tsaro, ta hanyar gabatar da sharhin Dokta Cemil Doğaç na tsangayar harkokin duniya ta jam’iyyar Atatürk da ke Türkiyya.

Kamfanin tsaro na Turkiyya ya ci babbar jarabawar a hare-haren yankin Afrin, na kan iyakar kasar da Sham.A 'yan shekarun da suka gabata,rashin kwanciyar hankali a kasashe makwabta, da kuma shiga tsakanin da sojojin Turkiyya ke ci gaba da yi a yankuna da dama,yasa bukatar sabuwar fasahar yaki ta kunno kai.Turkiyya na ci gaba da yin kacibus da manyan matsaloli kala daban-daban.Abinda yasa samar da yawan nagartattu fasahohi, dabarun yaki da kuma bukatar karfafa gwiwar bataliyoyin sojan Turkiyya ta kara daduwa.

A 'yan shekaru 15 da suka shude, yawan makamai da kayayyakin yaki kirar Turkiyya da aka fitar zuwa kasashen waje,ya ninka kusan sau 15, sojojin Turkiyya kuma, sun zabi fifita makaman da aka kera a masana'antun kasarsu,wanda hakan yasa aka samu muhimmin cigaba.Daga shekarar 2013 ya zuwa yau, kamfanonin tsaro 450 na kasar Turkiyya ne, suka fitar da makamai zuwa kasashen waje 177.

A bara, masana'antun tsaron Turkiyya sun yi cinikin dalar Amurka biliyan 2,inda kamfanonin jiragen saman kasar, suka siyar da makaman da farashinsu ya haura dalar Amurka biliyan 6.Turkiyya wacce a shekarar 2002, ta saye kashi 80 cikin dari na makamanta daga kasashen waje,a yau, kashi 35 a cikin dari na makaman da take amfani da su ne kawai,suka fito daga ketare.

Kera ababen hawa masu sulke,makamai masu linzami wadanda ke iya cin matsakaici da kuma dogon zango,jiragen sama marasa matuki,jiragen ruwa na yaki da kuma isassun harsasai, abu ne muhimmi a fannin tsaron kasa, musamman ma ga kasar da ke son kubuta daga yin dogaro da kasashe waje.Babban abun da ya haifar da wannan cigaban shi ne, kunnen uwar shegun da masu sayar wa da Turkiyya makamai suka yi, a wajen kin cika alkawurransu, sabili da manufofin siyasa da kuma nuna rashin amincewarsu, dangane da batun bunkasa fasahar kera makamai a Turkiyya.

A daidai lokacin da shugaban Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa "Mun zamo bakon mugun makwabci",Turkiyya ta shiga sahun kasashen da suka yi matukar ci gaba a fasahar tsaron kasa da ta kera makamai, da kafar dama.Duba da yarjejeniyoyin kasa da kasa,kamata yayi abokan ittifakin Turkiyya, a karkashin tutar Majalisar Dinkin Duniya da ta NATO, su tabbatar da tsaro a Turkiyya.Amma rashin cika alkawurra,kin yin amfani da tsarin kare dangi don amfanin Turkiyya,da kuma yi wa bukatar Turkiyya ta samar da nargattatun ababen hawa na sama da kasa zagon kasa,yasa matsalar rashin yarda da juna ta kunno kai tsakanin Turkiyya da kawayenta.

A yau,A mastayin da ake, a jerin sunayen manyan masana'antun tsaro na duniya,wanda aka yi wa take da “Defense News Top 100”, akwai kamfanoni Turkiyya 3.Masana'antun Turkiyya na ci gaba da samun odar kayayyaki yaki daga sassa daban-daban,duba yadda suka nuna bajinta da kuma kwarewarsu a kurwowi 4 na duniya.A baya-bayan nan,Turkiyya ta rattaba hannu a wasu takardu don sayar wa da Pakistan, jiragen masu saukar ungulu, wadanda ake amfani da su a wajen kai farmakai da yin sintiri,a yayin a daya gefe , zata siyar wa Maleshiya jiragen sama marasa matuki.

Tuni aka fara kera tankokin yaki samfurin Altay, wadanda suka yi matukar amfanarwa ga sojojin Turkiyya a farkaman tsarin tsaro na Firat.Haka zalika ana ci gaba da aiyukan kera injinan wadandan ababen hawan, a Turkiyya.A shekarar 2020, ana hasashen fara kera makamai masu linzami wadanda ke cin matsakaici da kuma dogon zango, samfurin Atılgan da Zıpkın, a albarkacin sabon tsarin bunkasa fasahar Hisar-A.

Jiragen masu saukar ungulu da ababen hawa marasa matuki wadanda ake iya amfani da su a wajen safara da kuma harba rokoki, sun nuna wa Sojojin Turkiyya muhimancinsu a albarkacin hare-haren Reshen Zaitun.Amma ga dukannin alamu, akasin yadda ake zaton cewa, Turkiyya zata yi amfani da makaman da ta kera, ba tare da ta yi odar daida da karfe daya daga ketare ba,tsarin ne da zai dauki tsawon lokaci.Domin dole ne Turkiyya ta daura damara a wajen warware matsalolin da ke gabanta,musamman ma wadanda suka jibanci tanadar isassun kudade da kuma zurfafa sani a bangaren fasahar yaki.Wannan kuma, abu ne da zai dauki lokaci mai matukar tsawo.Haka zalika,sanin kowa ne a yau akwai alaka tsakanin kusan dukannin kasashen duniya,wanda a ciki har da kasashen da suka zarce a fannin soja.

A duk fadin duniya kasashen Amurka da Rasha ne kawai ba su dogara da kowace kasa ba.Idan muka dubi tattalin arziki da kuma cigaban fasaha,da wuya Turkiyya ta goga da wadannan kasashen, a cikin kankanin zamani.

Shi yasa,bai kamata ba,manufar Turkiyya ta bai wa masana'antunta damar kera makamai masu limzami ta hanyar yin amfani da fasahar 'yan kasarta, ta kasance ta gino kan kajeren zamani. ya ci a ce wannan tsari ne na matsakaici da kuma dogon lokaci.

Domin manufar da aka gina kan gajeren zamani, aba ce da ke da wuyar tabbatuwa, haka zalika zata haifar da babbar matsalar tattalin arziki.A gefe daya kuma,matsakaiciya ko kuma doguwar manufa,zata iya bai wa Turkiyya damar cimma burinta a yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya ga baki daya.

Mun gabatar muku da sharhin Dokta Cemil Doğaç na tsangayar harkokin duniya ta jam’iyyar Atatürk da ke Türkiyya.Labarai masu alaka