Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya yi wa jama'a jawabi a lardin Erzincan ında inda ya soki Amurka da kakkausar murya game da taimakon da ta ke ba wa 'yan ta'addar YPG. Ya ce, a yanzu Amurka ta ci karo da bango, wannan ba abu ne mai sauki ba.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Sakatare Janar na Rundunar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya yi sharhi game da hare--haren Reshen Zaitun da Turkiyya ke kai wa a Afrin inda ya ce, kasar na da damuwa game da ta'addanci kuma babu wata kasa mamban NATO da ta fuskanci hare-hare kamar Turkiyya.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Mataimakin Firaministan Turkiyya Mehmet Şimşek ya bayyana cewa, nan da wata Yuni za a kammala gyaran tsarin bayar da bashi da kudaden kasashen waje ga kamfanunnuka. Şmşek ya tattauna da Bloomberg inda ya ce, samar da asusu daya ba yana nufin akwai matsalar tattalin arziki ba ne.

Babban labarin jaridar Huriyet na cewa, kama gidajen otel da aka yi a Jamus don zuwa Turkiyya yawon bude ido ya karu da kaso 50 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Ana sa ran 'yan yawon bude ido a bana a Turkiyya za su haura na shekarar bara sosai. Mai Bayar da SHawara Kan sha'anin yawon bude ido a Berlin Huseyin Gazi Coşan ya ce, Turkiyya ta sake dawo wa kasuwar Jamus. Adadn wadanda za su ziyarci Turkiyya a bana don yawon bude ido a lokacin zafi za su haura na bara sosa.Labarai masu alaka