Ana jiran tashin rana,sai ga ranaku 3 sun tashi

Mazauna St. Petersburg na kasar Rasha ta shaida wani abin ta'ajibi da ya afku a garinsu,inda a yayin da suke jiran fitowar rana,sai ranaku 3 suka bullo a sararin samaniya.

An kira wannan lamarin wanda ya wakana a cikin matsakaicin lokaci da suna "Makaryaciyar Rana", a yaren Latin kuma ana kiran sa "Parhelia".

An tabbatar da cewa, wannan wani abu ne wanda daman ya saba afkuwa lokaci zuwa lokaci a wasu sassan duniya, kuma ya samo asali ne daga haskawar rana kan wata dunkulalliyar kankara wacce  ba a iya gani da ido.Abinda yasa rana ke bullowa a samaniya tamkar 3.

 Labarai masu alaka