Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Kasar Turkiyya.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star na cewa, A cibiyar Kasa ta Katar an fara Kasuwar baje-Kolin Kayan Tsaron Ruwa na shekarar 2018 (DIDEX2018). Ministan Tsaron Turkiyya Nurettin Canikli da SHugaban RUndunar SOjin kasar Janar Hulusi Akar, Mai Bayar da Shawara a Turkiyya ka Kamfanunnukan Samar da Kayan Tsaro Isma'il Demir sun halarci bikin bude kasuwar. Akwai kamfanunnukan Turkiyya 33 karkashin Kungiyar Fitar da Kayayyakin Tsaro ta Kasar da ke halartar Baje-Kolin. Wajen da ake gabatar da baje-kolin ya kai girman mika sukwaya dubu 2,413.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Manyan jiragen ruwa na duniya sun mayar da hankalinsu zuwa Turkiyya. Sanarwar da Kungiyar 'Yan kasuwar yankunan Istanbul da Marmara, Aegean, mediterrenean da Black Sea suka bayar na cewa, sun gana da manyan kamfanunnukan jiragen ruwa na Amurka a tsakanin ranakun 5-8 ga watan Maris. An bayyana cewa,sun tattauna abubuwa masu kyau da kamfanin Seatrade Cruise Globalna Florida da ke shirya baje-koli. An amince da gudanar da baje-kolin 2019 a garuruwan ızmir da Antalya na Turkiyya.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Turkiyya ta fara daukar mataki game da rahoton abun kunya da Hukumar Moody me auna darajar basussuka ta yi game da Turkiyyan a makon da ya gabata. A wannan shekarar Turkiyya za ta kafa tata hukumar mai auna darajar basussukan kasashen duniya.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Adadin Fasinjojin da Kamfanin Jiragen Saman Turkish Airlines ya dauka a watan Fabrairun 2018 ya karu da kaso 26 cikin dari idan aka kwatanta ahi da na watan Fabrairun 2017 inda ya kama mutane miliyan 5.1.Labarai masu alaka