“Mun shirya fuskantar komai,ko mu yi shahada ko dai mu yi nasara”

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan  ya bayyana cewa,komai wuya komai rintsi,ba za su taba kasa a gwiwa ba wajen ganin bayan dukannin wadanda suka tunkari Turkiyya da kunshin fitina, sharri da na kulle-kulle.

“Mun shirya fuskantar komai,ko mu yi shahada ko dai mu yi nasara”

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan  ya bayyana cewa,komai wuya komai rintsi,ba za su taba kasa a gwiwa ba wajen ganin bayan dukannin wadanda suka tunkari Turkiyya da kunshin fitina, sharri da na kulle-kulle.

Erdoğan wanda yayi jawabi a yayin taron  jam’iyyar AKP (Jam’iyyar Adalci da Cigaba) karo na 6,wanda aka shirya a rufaffen filin motsa jiki na gundumar Serdivan da ke Turiyya,ya ce :

“Kamar yadda muka kai ruwa rana wajen yi wa kasarmu hidima, haka muke ci gaba da safa da marwa don ganin mun share kwallan Musulmai a duk inda suke a doron duniya.Muna fadi tashin kai wa ‘yan uwanmu na Afirka da na kudancin Asiya dauki.A duk tsawon tarihinmu, kama daga daular Usmaniyya zuwa Jamhuriyyar Turkiyya, ba mu taba mulkar wata kasa don handame arzikinta ko kuma yi wa al’umarta kisan gilla ba.Ba mu taba zubda jinin wani bawan Allah don wata manufa tamu, ko don zinare, lu’ulu’u,da kuma man fetur”.

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa :

“Amma duk wanda ya nuna mana yatsa, ya tunkare mu da manakisa da shirin raba kanun al’umarmu,yunkurin hargitsa karsarmu,ko kuma maida kasarmu tamkar gulbin jini,to ko shakka babu sai ya yaba wa aya zakinta.Turkiyya na fatan tabbatar da adalci, ‘yanci,tsaro da kuma dogaro da kai ga ga illahirin kasashen duniya.Komai wuya komai rintsi,ba za mu taba kasa a gwiwa ba wajen ganin bayan dukannin wadanda suka tunkari Turkiyya da kunshin fitina, sharri da na kulle-kulle.Mun shirya fuskantar komai,ko mu yi shahada ko dai mu yi nasara".

 Labarai masu alaka