Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar HaberTurk na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu da ke ziyara Moscow Babban Birnin Kasar Rasha ya bayyana cewa, a ranar 19 ga watan maris za su gana da Amurka kuma za su cimma matsaya game da Munbich. Minista Cavusoglu ya ce, idan reshen 'yan ta'addar PKK da ke Siriya YPG suka janye daga Munbich to sojojin Amurka da na Turkiyya za su kula da wajen.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Turkiyya ta la'anci harin da aka kai wa Firaministan Falasdin Rami Al-Hamdallah a zirin Gaza a lokacin da ya ke tafiya tare da jerin gwanon motocinsa. Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta la'anci harin tare da Addu'ar samun sauki ga wadanda suka jikkata. Haka zalika Turkiyya ta bukaci da a nemo maharan cikin gaggawa. Sanarwar ta kuma ce, Turkiyya na tare da 'yar uwarta Falasdin a wannan yanayi da ta shiga. 

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Kungiyar Hadin Kan Cigaban Tattalin Arziki ta DUniya OECD ta fitar da rahotonta na watanni 3. Rahoton ya ce, Tattalin Arzikin Turkiyya ya habaka da kaso 6.9 a shekarar 2017 wanda ya kasance 6.1 a 2016. haka zalika a 2018 aa sa ran zai habaka da kaso 5.3 sai a 2019 da zai habaka da kaso 5.1

Babban labarin jaridar Star na cewa, Kamfanin Samar da Kayan Jiragen Ruwa na OES da ke aiki a Mersin ya fara aiyukan samar da jiragennruwa marasa matuki. Za a samar da jiragen da kayan cikin gida kuma nan da shekara 1 za a kammala aikin.

 Labarai masu alaka