"Ya kamata mu yi alfahari da Turkiyya,al'umarta da kuma yarenta"

Shugaban kasar Farisa Hasan Ruhani ya ce Turkanci yare ne da ya kamata al'umomin Gabas ta Tsakiya su yi alfahari da shi.

"Ya kamata mu yi alfahari da Turkiyya,al'umarta da kuma yarenta"

Shugaban kasar Farisa Hasan Ruhani ya ce Turkanci yare ne da ya kamata al'umomin Gabas ta Tsakiya su yi alfahari da shi.

Shugaban na Iran ya ce

"Turkanci abin alfahari ne kasashen yankinmu, filawa ce daga furennin masu kanshi"

A cewar bayanin da fadar shugaban Iran ta wallafa a shafinsa na intanet,shugaban na Iran wanda ya yi jawabi a filin wasannin motsa jiki na garin Tebriz inda ya kai ziyara,Ruhani wanda ya ke yiwa al'umarsa jawabi yace yada yaren Turkanci abu ne mai matukar muhimmanci.

Ruhani, Türkçe için gerekli kitapların basılması talimatı verdiğini belirterek,

Don koyar da Turkanci, Ruhani ya bada umarni da gaggauta bugun litattafan da suka dace kana ya ce,

"Saboda Turkanci abun alfahari ne na kasashen wannan yankin da muke ciki, haka zalika filawa ce daga furenni masu matukar kanshi.Mu ma kamata ya yi mu yi alfahari da kasar Turkiyya da al'umarta da kuma yarenta".

Wadannan kalaman na Ruhani sun zo ne kwanaki 2 bayan da wakilai Turkawa na majalisar Iran suka tada jijiyoyin wuya kan furucin da mataimakinsa Ali Yunusi ya yi na cewa "Azeriyawa Farisawa ne masu magana da Turkanci".

A ranar Jumma'a Turkawan iran sun yi Allaha wadai da matakin da kasarsun ta so dauka na ganin an koyar da yaren Rashanci a makarantun kasarsun a yayin za a koyar da Farisanci a makarantun Rasha.

 Labarai masu alaka