Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 18.06.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 18.06.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 18.06.2018

Babban labarin jaridar Star na cewa Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da wani sako a ranar 18 ga watan Yuni domin tuna gayowar ranar kafa Rundunar Sojin Ruwan Kasar inda ya ce, Rundunar Sojin Ruwanmu za ta ci gaba da faranta mana tare da kara karfin rundunar tsaronmu.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Ministan Masana'antun da Fasahar Kere-Kere na Turkiyya Faruk Ozlu da ya bayyana cewa, masu son sayen motocin da aka kera a Turkiyya sun shirya ya sake cewa, an gama sayen motocin na gida da za a samar. Da a ce za a fitar da su kasuwa a yanzu da an samu miliyoyin mutane da suka nuna bukata.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, an ba kamfanunnuka 80 waje a Tsararren Yankin Kafa Masana'antun Kera Kayayyakin Jiragen Sama a birnin Ankara na Turkiyya inda aka kuma sanya hannu da wasu kamfanunnukan 40. Mutane dubu 15 ne za su samu aiki a karkashin shirin.

Babban labarin jaridar Star na cewa, a lokacin hutun Sallah Karama gidajen otel da ke kusa da Kizkalesi da ya shiga jeri sunayen wuraren al'adu da tarihi na Hukumar Bunkasa da Ilimi da Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) sun cka makil da jama'a.Labarai masu alaka