Turkiyya za ta gina katabaren cibiyar kimiyya da fasaha a Istanbul

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar Turkiyya za ta gina katabaren cibiyar kimiyya da fasaha da mutane miliyan biyu za su rinka ziyarta a ko wacce shekara.

Za’a dai gina cibiyyar ce a sashen Nahiyar Turai dake birnin Istanbul, a inda kuma za’a rinka kirar cibiyar da sunan “Golden Horn”.

Shugaba Erdoğan ya bayyana hakan ne a shafinsa ta twitter inda ya nanata cewar cibiyar  da za’a kammala cikin shekaru uku za ta kai girman sikwaya mita 800 kuma za’a kashe dala miliyan 21 wajen gina ta.
 Labarai masu alaka