Amurka ta fara mika wa Turkiyya jiragen yaki samfurin F-35

Kasar Amurka ta fara mika wa Turkiyya jiragen yaki samfurin F-35 wadanda suka tanadi ingatacciyar fasahar tsaro, kyamarori masu hangen nesa da maganadisun radar.

Amurka ta fara mika wa Turkiyya jiragen yaki samfurin F-35

Kasar Amurka ta fara mika wa Turkiyya jiragen yaki samfurin F-35 wadanda suka tanadi ingatacciyar fasahar tsaro, kyamarori masu hangen nesa da maganadisun radar.

An shirya bikin karbar jirgi na farko,wanda aka kera karkashin tsarin bai-daya na samar jiragen yakin samfurin F-35 na Amurka da sauran kasashen duniya,a ciki har da Turkiyya, a farfajiyar filin Lockheed Martin da ke yankin Teksas-Fort Worth.

A bikin an samu halartar ministocin tsaron kasashen Amurka da Turkiyya, dukannin wadanda suka yi ruwa da tsaki a wannan aikin, da manyan shugabannin Lockheed Martin.

 Za a aika jirgin mai lambar 18-0001 zai kasance a sansanin sojin Amurka da ke yankin Arizona don gudanar da atisaye.

Wannan abun hawan ya kasance jigin yaki mafi ingancin da nagarta.

A 'yan kwanakin nan Turkiyya za ta karbi jirginta na 2, a watan Maris na 2019 jirage na 3 da na 4.

Jiragen zasu kasance a Amurka a tsawon lokacin da za a horas matuka.

Bayan an kammala kera su, jirage na 5 da na 6 za su kasance a Turkiyya a Nuwambar shekarar 2019.

A twason shekaru,Turkiyya za ta mallaki a jimillance jiragen yaki samfurin F-35 da 100.

Turkiyya ta kasance a tsarin bai-daya na samar da jiragen f-35 tun a shekarar 1999,inda ma'aikatar kera makamai kasar ke ci gaba da taka rawar a zo a gani.


Tag: amurka

Labarai masu alaka