Ana bincike a gidan jakadan Saudiyya da ke Istanbul

Masu bincike na Turkiyya da suka hada da yan sanda na gudanar da bincike a gidan jakadan Saudiyya da ke Istanbul.

Ana bincike a gidan jakadan Saudiyya da ke Istanbul

Masu bincike na Turkiyya da suka hada da yan sanda na gudanar da bincike a gidan jakadan Saudiyya da ke Istanbul game da dan jarida Jamal Kashogghi da ya bace tun ranar 2 ga Oktoba.

Ana gudanar da binciken a gidan jakadan bayan daukar awannin 9 ana gudanar da wani binciken a ofishin jakadancin Saudiyya da le Istanbul.

Ama tunanin an samu wasu alamu a irin samfurin da aka samu a binciken da aka yi a ranar Litinin din nan. 

Jakadan Saudiyya da le istanbul ya koma kasarsa da karfe 5 na yammacin wannan rana.

Tun 2 ga Oktoba dan jaridar Washington Post Jamal Kashogghi ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya inda har yanzu ba a sake samun labarin sa ba Labarai masu alaka