Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 16.10.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 16.10.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 16.10.2018

Babban labarin jaridar Star na cewa, a lokacinda Turkiyya ke mayar da hankali kan habaka tattalin arzikinta, a gefe guda kuma tana daukar nauyin muhimman aiyuka a Hukumomin Kasa da Kasa. A karkashin haka a yanzu Turkiyya ta karbi jagorancin gudanar da aiyukan Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF inda za ta rike mukamin Daraktan Gudanarwa har nan da shekarar 2020 a IMF din.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a lokacin da ake ci gaba da aiyukan kokarin kaddamar da filin tashi da saukar jiragen sama na 3 da ke Istanbul a ranar 29 ga Oktoba, a gefe guda kuma ana ci gaba da gwaje-gwajen tashi da sauka. A wannan gwajin da ake yi jiragen fasinjoji na Turkish Airlines guda uku za su sauka a filin. Bayan jiragen sun sauka za a kusantar da su ga gadoji sannan a ajje motocin daukar kaya a kusa da su.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, ana ci gaba da aiyukan daga gine-ginen masanaa'antar samar da makamai a yankin Kirikkale na Turkiyya a waje mai girman kadada 500 wanda shi ne irin sa na farko a kasar. A ranar 15 ga watan Fabrairun 2019 za a fara samar da makamai a masana'antar. Shugaban kamfanin sarrafa makamashi mai suna "Synergy Energy Systems"Adnan Duman ya ce, su ne za su samar da manyan bangarorin bindigun da za a samar saboda kamfaninsu wani bangare ne ko kuma ya samu amiincewar Hukumar Kula da Kera Injina da Sarrafa Makamashi a Kimiyyance. Ya ce za su samar da bindigu samfurin MPT-76 da MPT-55 sannan baya ga su akwai wasu da dama da za su samar.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Can Oncu da ya yi nasara a gasar tseren babura ta MotorGP inda ya lashe kofin "Red Bull Rookies Cup", ya zama na biyu a gasar matasa ta tsere ta duniya karo na 7 ta FIM da aka yi a Spamniya. A ranar 25 ga watan Nuwamba za a yi tseren karshe na gasar ta matasa a Spaniya.Labarai masu alaka