Naman kajin da aka lullube da zinare ya samu karbuwa a Amurka

Naman kajin da aka barbada wa garin zinare mai nauyin karat 24,wanda a yanzu aka fara gabatar wa jama'a da shi a wasu daidaikun gidajen cin abinci na New York, ya samu karbuwa sosai a Amurka.

Ana siyar da nama kajin tare da miyar markadadden borkono,dunkule da man kwakwa.

Bayan an gama soya kajin,sai a barbada musu garin zinaren kafin a yi wa kwastomomi bismillah.

Ana siyar da wannan abincin a dalar Amurka 45,watau kusan Naira dubu 17,000. Jama'ar Amurka sun yaba wannan abincin. A yanzu haka sunan wannan girkin ya kasance a jerin sunayen dafe-dafen gidajen cin abinci na birnin Manhatan guda 2.