“Kaddara ta yi wa Eboue daurin gwarmai”

Rayuwar shahararren mai taka leda na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal,Emmanuel Eboue ta koma rana zafi inuwa kuna,tun bayan aran na kare da makuden milyoyi da kuma ‘ya ‘yansa, da Baturiyar maidakinsa ta yi,ba tare da ta bar masa ko kwandala ba.

“Kaddara ta yi wa Eboue daurin gwarmai”

Rayuwar shahararren mai taka leda na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal,Emmanuel Eboue ta koma rana zafi inuwa kuna,tun bayan aran na kare da makuden milyoyi da kuma ‘ya ‘yansa, da Baturiyar maidakinsa ta yi,ba tare da ta bar masa ko kwandala ba.

A watannin da suka gabata,dan wasan kwallon kafan ya bayyana wa duniya cewa,ya tsunduma halin ha-ula-i,sakamakon iftali’in da ya yi masa bazata,inda yake ci gaba da gudun hijira daga wannan loko ya zuwa wancan unguwa,don guje wa jami’an tsaro da kuma lauyoyi.

 Eboue ya ce:

 “Akasin yadda na dinka wadaka da dukiya a baya, a yanzu a kasa nake kwanciya,kana ko abincin da zan saka a bakina na yi mun wuya.Bani da ko kwabo.A gaskiya,idan na tuna irin yadda na taka rawar a zo a gani a kungiyoyin kwallon kafa na Arsenal da Galatasaray,sai zuciyata ta dinka kuna.’Yan uwa da abokai sun juya mun baya. Ina fama da matsanancin kadaici.Wannan wani lamari ne mai matukar wuya,wanda na saba gani a fina-finai.Amma sai kuma kwatsam na tscinci kaina a ciki,kamar a mafarki”.

Daga karshe mashahurin dan wasan ya ce :

”A yanzu ba ni da wata bukata wacce ta wuce in sake rungumar sana’ata.Saboda ina son kwallon kafa,kuma sai na ga abinda ya ture wa buzu na nadi a wajen tabbatar da burina na komawa filin wasa.Ban damu ba,idan Pakistan ko Bagadaza za a kai ni,ni dai in taka leda”.

 

 

 Labarai masu alaka