Kanfanin wayar Samsung ya tsokani Koriya ta Arewa da Iran

Kanfanin wayar tarhon Samsung da ke Koriya ta Kudu ya yi alkawarin baiwa dukkan 'yan wasan da za su halarci wassanin Olympics a kasar wayar tarho amma banda 'yan wasan Koriya ta Arewa da na Iran, lamarin da ya janyo kace-nace tsakanin kasashen.

Kanfanin Samsung din da ya yi alkawarin rabawa dukkan jagorori da 'yan wasan Olympics da za'a gudanar a Koriya ta Kudu ta bada sanarwar cewa ba za ta baiwa 'yan kasar Koriya ta Arewa da Iran ba saboda suna karkashin takunkumin Amurka.

Wanan lamarin ya sanya kasar Iran daukar mataki inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Behram Kasımi ya bayyana cewar idan kanfanin Samsung ba ta janye wannan mataki na ta ba, ta kuma bada hankuri hakan zai janyo ma ta samun matsalar kasuwanci a kasar ta Iran.

A dayan barayin kuma shugaban kwamitin tattalin arzikin kasar Iran Ali Ekber Kerimi ya yi kira ga al'ummar kasar Iran dasu daina sayen kayayyakin kanfanin Samsung din.

Hukumar kanfanin Samsung za ta raba wayoyi dubu 4 ga 'yan wasa a taron wasannin hunturun da za'a gudanar tsakanin 9-25 ga watan Fabrairun 2018 a garin PyeongChang dake Koriya ta Kudu.

 Labarai masu alaka